Bayan da ya samu lambar yabo ta zaman lafiya ta “Noble” ta bana, fira ministan kasar ta Habasha Abiye Ahmad yana fuskantar wani sabon kalubalebayan kashe mutane 67 a wata Zanga- zangar da aka gudanar a makon da ya gabata,kana yayi tir game da matakin tsokana da wasu ke yi don neman haddasa da rikicin addini da na kabilanci a kasar.

Har ila yau ya bayyana fargabarsa ta yiyuwar yaduwa rikicin matukar alummar kasar ba su hada kansu ba, yana mai cewa za su dauki tsauraran matakai da suka dace wajen ganin an kawo karshen rikicin tare da tabbatar da adalci da kuma gurfanar da duk wanda ke da hannu wajen rikicin a gaban kotu domin hukumta su.

A ranar Laraba da ta gabata ce rikici ya barke a babban birnin kasar Adis Ababa, kafin ya yadu zuwa yankin Orumiya inda magoya bayan dan rajin kare hakkin dan Adam din nan Jawar Mohammad suna hau kan tituna tare da kona tayoyi a kan tituna da kuma toshehanyoyin dake isa zuwa sauran birnanan kasar.

Babban jami’an yan sanda a yankin na Oromia ya bayyana cewa mafi yawancin wadanda suka rasa rayukansu sun mutu ne sakamakon arangama tsakanin masu Zanga- zangar tun kafin a aike da jamian ‘yan sanda zuwa wajenda rikicin ya yi kamari domin tabbatar da tsaro.