A daren jiya talata firai ministan kasar Pakistan Imaran Khan ya gana da sarkin kasar Saudiya Salman bin Abdul-Aziz da kuma Muhamad bin salman yarima mai jiran gado a gebance.

Yayin da ya kai ziyara kasar Saudiya firai ministan kasar Pakistan Imran Khan ya gana da sarki Salman bn Abdul-aziz a birnin Riyad, inda suka tattauna kan mahiman batutuwan da ke faruwa a yankin gabas ta tsakiya da kuma fadada alaka tsakanin biranan Islamabad da Riyad.

A bangare guda kuma, firai ministan na kasar Pakistan ya gana da yarima mai jiran gado na Saudiyar Muhamad bn Salam, inda suka tattauna kan hanyoyin da ya kamata a bi domin magance rikicin yankin gabas ta tsakiya da kuma fadada alaka tsakanin kasashen biyu.

A jiya talata ce firai ministan na kasar Pakistan ya jagoranci wata babbar tawagar kasar zuwa kasar Saudiya, kuma wannan shi ne karo na uku da firai ministan ke kai ziyara zuwa kasar Saudiyar cikin wannan shekara da muke ciki.

Duk da cewa ba a bayyana mahiman batutuwan da aka tattauna kansu ba, to amma ana tunanin cewa firai ministan na Pakistan ya isar da sakon mahukuntan birnin Tehran ne zuwa ga na birnin Riyad, ganin cewa a ranar lahadin da ta gabata ya kawo ziyara birnin Tehran tare da ganin an warware matsalar dake yankin gabas ta tsakiya.