Firaminsitan kasar Habasha, Abiy Ahmed, ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya ta shekara 2019.

Dan shekara 42, Abiy Ahmed, an jima ana kallonsa a matsayin mai fafatukar samarwa kasarsa ta Habasha zaman lafiya.

Mista Ahmad, shi ne wani firaminista na farko da aka samu a kasar daga ‘yan kabilar Oromo, kuma a karkashin gwamnatinsa ne kasashen Habasha da Erytrea suka kulla zaman lafiya a ranar 9 ga watan Yuli na 2018, bayan shafe shekaru ashirin na zaman tankiya, kan iyakar dake tsakaninsu.

Rikicin kasashen biyu wanda ya kai ga barkewar yakin basasa a tsakanin shekara 1998 zuwa 2000 ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 80,000