A yau litinin ne ake sa ran majalisar dokokin kasar za ta zauna domin amincewa da sabon shirin da Firaministan kasar Sa’ad Hariri ya gabatar na yin garanbawul da hakan zai kawo karshen Zanga- znagar da aka kwashe kwanaki 4 ana yi a kasar.

Daga cikin abubuwan da shirin ya kunsa akwai batun rage kashi 50% na albashin manyan jami’ain gwamnati na yanzu da wadanda suka gabata, da kuma taimakawa bankuna da kudidala biliyan 3.3 da zai taimaka wajen cike gibin da ake da shi a kasafin kudin shekara ta 2020 mai kamawa.

Kuma za’a sayar da ma’aikatar sadarwa ta kasarga yan kasuwa.

Wannan mataki yana zuwa ne adaidai lokacin da wa’adin da Firaministan ya ba wa mukarraban gwamnati na saoi 72 yake gab da cika.

A nasa bangaren babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hassan Nasrullah ya ce yana adawa da duk wani yunkurin rusa gwamnatin kasar, kuma ba za su taba amincewa da wasu su kona kasar tare da haifar da rikici ba. Ya kara da cewa zamu yi aiki tukuru wajen ganin an warware matsalar da kasar ke ciki, ba za su bari wasu su jefa ta cikin rami ba.