Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Firministan kasar Habasha ya ce kasarsa a shirye take ta yi yaki da kasar Masar
Abi Ahmad wanda kwanaki 12 da su ka gabata aka sanar da shi a matsayin wanda ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya, ya yi gargadin cewa; Idan har bukatar yaki ta taso akan madatsar ruwan “millineum” to kasarsa a shirye take.

Sai dai firaminstan na kasar Habasha ya ce; Kasar tasa ta fifita tattaunawa a matsayin hanyar warware sabani.

Kasashen biyu dai suna da sabani da juna akan madatsar ruwan da Habasha din take ginawa saboda zai rage kwararar ruwa zuwa tekun maliya kamar yadda Masar ta yi zargi.

Ana sa ran cewa firaminstan na Habasha Abi Ahmad da kuma shugaban kasar masar Abdufattah al-sisy za su gana da juna a yayin taron da kasashen Afirka za su yi da kasar Rasha daga yau zuwa gobe.

Abi Ahamd ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya saboda rawar da ya taka na kawo karshen yaki tsakanin kasarsa da Eritrea.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu