A yau Alhamis an sanar da mutuwar giwaye fiye da 100 saboda fari da kuma bullar cutar bakon dauro.

Binciken farko da aka gabatar ya nuna cewa; giwayen sun mutu ne saboda bullar fari a yankin da kuma yaduwar cutar bakon dauro a tsakanin dabbobin na daji.

Wata hukuma wacce take kula da dabbobin daji ta bayyana cewa; Daga shekarar 2014 zuwa 2018 an sami raguwar giwaye da kaso mai yawa, mafi yawanci saboda faruatarsu da ake yi ba bisa ka’ida ba, sai kuma fari.

A kwanakin baya ma an bayyana cewa wasu giwayen fiye da 50 sun kwanta dama a kasar Zimbabwe.