Tawagar gwamnatin kasar Yemen ta gana da jakadan kasar Birtania a kasar Yemen inda su ka tattauna batutuwan da su ka shafi zaman lafiya da ayyukan ceto da agaji a cikin kasar Yemen.

Jagoran tawagar ta kasar Yemen, Muhammad Abdussalam ya ce; daga cikin batutuwan da bangarorin biyu su ka tattauna da akwai batun tsagaita wutar yaki da shugaba al-Mushad ya gabatarwa kasar Saudiyya a ranar 21 ga watan |Satumba da ya shude.

A nashi gefen, jakadan kasar Birtania a Yemen, Micheal Aron ya yaba da tayin tsagaita wutar yakin da gwamnatin ta Yemen ta gabatar tare da bayyanata a matsayin dama domin shimfida zaman lafiya