Yarjejeniyar kuma za ta bayar da damar shigar da taimakon jin kai zuwa yankunan da aka dade ana gwabza yakin basasa na fiye da shekaru takwas.
An kulla wannan yarjejeniyar ce a Sudan ta Kudu, kuma kungiyoyin 'yan tawaye daga Darfur da na Nuba da wadanda ke yankin kogin Blue NIle sun halarci bikin.
A makon jiya, gwamnatin Sudan a Khartoum ta ayyana tsagaita wuta a dukkan yankuna ukun.
Wannan gwamnatin ce ke tafiyar da mulkin kasar - tun bayn hambare gwamantin Omar al Bashir a watan Afrilun bana - kuma ta lashi takobin hada kan kasar.