Majiyar gwamnatin kasar Siriya ta bayyana cewa gwamnati ta fara tura rundunonin sojoji ta zuwa arewacin kasar don dakatar da sojojin Turkiya wadanda suka fara mamayar kasar a ranar Laraban da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Siriya SANA ya bayyana cewa sojojin sun fara shiga yankunan kurdawa wadanda mayakan kungiyar SDF suke iko da su a jiya, bayan wata tattaunawa tsakanin kungiyar da gwamnatin kasar.

Har’ila yau labarin ya kara da cewa sojojin na Siriya tare da kawayenta na kungiyar Hizbullah da sauransu zasu dakatar da kutsawar da sojojin Turkiya da kuma kawarta ta kungiyar yan ta’adda ta Jaishul Hur suke yi daga arewacin kasar ta Siriya
Ahmed Sulaiman, wani jigo a cikin kungiyar kurdawa ta KDPP ya shaidawa Reuters cewa kungiyar ta fara tattaunawa da gwamnatin kasar Siriya kuma yana saran nan gaba kadan zasu cimma yerjejeniya da ita.