Firai ministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya bukaci mutanen kasar kada su bari rikicin da ke faruwa a cikin kasar a halin yanzu ya kara rikicewa.

Tashar talabijin ta “Channel 2” ta nakalti Ahmed yana fadar haka a jiya Asbar ya kuma kara da cewa gwamnatinsa zata zakulu wadanda suke da hannu a rikicin baya-bayan nan don hukunta su.

A ranar Laraban da ta gabata ce rikici ta barke a birnin Adisababa babban birnin kasar da kuma yankin Oromia, bayan da wasu yan adawa suka yi kokarin jagorantar wata zanga-zangar na yin allawadai da shi.

Ya zuwa yanzu dai an kashe mutane akalla 67 tun bayan barkewan rikicin.

Ofishin Firai ministan ya kammala da cewa wasu masu adawa das hi suna son maida rikici ya zama na kabilanci da kuma addini.

Abiy Ahmed dai yana da cikin wadanda aka zaba don samun kyautar Nebel ta zaman lafiya na wannan shekara ta 2019.