Ismaila Haniya shugaban kungiyar Hamas ta Paladinu ya bayyanacewa makarkashiyar raba masallacin kudus ba zai yi nasara ba, kuma ba za mu taba bari yan mamaya su aiwatar da mugun nufinsu ba na canza fasalin birnin kudus ko da zai kai ga sadaukar da dukkan rayukanmu ne.

Ya ci gaba da cewa duk da kalubale da muke fuskanta amma mun kama hanyar cin nasara, kana ya godewa dukkan palasdinawa da suka jajirci tare da yin tsayin daka wajen tunkarar gwamnatin mamaya ta HKI.

Idan ana iya tunawa a watan Disambar shekara ta 2017 ne shugaban Amurka Donald Trump ya amince da birnin Qudus a matsayin babban birnin HKI, kana kana ya daukeofishin jakadancin Amurka daga birnin Tel Avivzuwa birnin Qudus, lamarin da ya jawo Zanga- zanga a yankin Gaza domin nuna rashin amincewa da wannan mataki na yan mamaya.