Jagoran kungiyar Ansarullah sayyid Abdulmalik badruddin Alhouthi ya bayyana cewa, kaddamar da yaki kan al’ummar kasar Yemen ba shi ne zai kawo zaman lafiya a kasar da ma yankin gabas ta tsakiya ba.

Tashar Almasirah ta kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake ganawa da manzon musamman na majalisar dinkin duniya kan batun yemen Martin Griffiths jiya a birnin San’a, Jagoran kungiyar Ansarullah sayyid Abdulmalik badruddin Alhouthi ya jadda cewa, kaddamar da yaki da Saudiyya da kawayenta suke yi kan al’ummar kasar Yemen, shi ne ya jefa al’ummar kasar cikin mawuyacin halin da suke ciki.

Ya ce hanyar zaman lafiyaa kasar Yemen ita ce kawo karshen yakin da Saudiyya take yi da al’ummar kasar, kumaa kawo karshen killace kasar, tare da bude dukkanin iyakokin kasar, ta sama da kasa da kuma ruwa, tare da komawar dukaknin bangarorin siyasar kasar kan teburin tattauawa, tare da samun fahimtar juna a tsakaninsu.

Haka nan kuma ya gabatarwa manzon musamman na majalisar dunkiya shawarar yin musayar fursunonin yaki tsakaninsu da Saudiyya.

A nasa bangaren manzon musamman an mjalaisar dinkin duniya ya bayyana farin cikinsa matuka dangane da yadda ganawarsu da jagoran kungiyar Ansarallah (Houthi) ta kasace, tare da bayyana wadannan shawarwari da cewa za su taimaka matuka wajen kawo karshen yakin kasar.

Saudiyya dai tare da taimakon Amurka da kuma Birtaniya, ta kwashe kusan shekaru 5 tana lugudan wuta kan al’ummar kasar Yemen da sunan yaki da kungiyar Houthi, tare da kashe dubban fararen hula da suka hada da mata da kananan yara, da kuma rusa daruruwan masalatai, makarantu, asibitoci, kasuwanni da kuma dubban gidajen jama’a.

Majalisar dinkin duniya da kasashen duniya sun yi ta baiwa Saudiyya baki da ta kawo karshen yakin nataakan al’ummar kasar ta Yemen, amma tana yin biris da duk wadannan kiraye-kiraye tsawon kusan shekaru 5.

Amma bayan munanan hare-haren daukar fansa da mayakan na Yemen suka kai kan babban kamfanin mai na kasar ARAMCO akwanakin baya, da kuma kame dubban sojojin Saudiyya da ‘yan korenta a yankuna daban-daban da ke kan iyaka da Yemen,ahalin yanzu Saudiyya ta fara nuan alamun amincewa da kawo karshen yakin da take yi da al’ummar Yemen.