Wannan kungiya mai suna a sama a karo na uku sun sake gayyatar daya daga cikin 'yan'uwa malami a hauza dake birnin Qom Hujjatul Islami Dr. Shu'aibu Muh'd domin gabatar masu da lacca a fagen addini da rayuwa tare kuma da amsa tamboyi daga mahalarta taron wadanda su ma malamai ne a jami'o'i na ciki da wajen kasar Iran din.

Hujjatul Islami Dr. Shu'aibu ya sami rakiyar wasu 'yan'uwa a lokacin da zai tafi wannan taron.

Ya yi jawabai masu kayatarwa akan 1- Musulunci da siffa magamiya. 2- Shi'anci da yan shi'a a Najeriya, [musamman Harka islamiyya karkashin jagoranci Sayyid Zakzaki]. 3- sai kuma bayani akan ita kanta Najeriya [ta fuskar siyasa, addini ilimi,tsangayu dsr.] 4-sai kuma yankin yammacin Afrika.

Daga karshe mahalarta taron farfesoshi Daktoci da  manyan malamai sun rika yi masa tambayoyi yana amsawa.

A karshen sun karramashi da kyautar girmamawa inda daya daga cikinsu kuma makusancin Imam Khumaini tun kafin juyi ya mika masa kyautar tare da yi masa fatan alheri da godiya ta musamman a gareshi bisa amsa gayyata da kuma irin bayanan da suka ji.

Oct./2019.