Hukumar ta abinci ( FAO) ta fitar da bayani a jiya Laraba- da ake bikin ranar abinci ta duniya- inda ta yi gargadin cewa; Adadin mutanen da suke fama da yunwa yana karuwa a duniya kuma cikin gaggawa.

Sanarwar ta kara da cewa; Kaso 98 % na mutanen da adadinsu ya kai miliyan 800, suna fama da matsananciyar yunwa, kuma suna rayuwa ne a cikin kasashe masu tasowa.

A kowace ranar 16 ga watan Oktoba ne dai aka ware a matsayin ranar abinci ta duniya. Kasashe 150 na duniya kan hada hannu wajen wayar da kai dangane da talauci da kuma yunuwa.

Kididdigar da aka fitar tana nuni da cewa; Mutane miliyan 785 a duniyar nan, ba su da isassshen abinci kuma ba su rayuwa ma inganci ta fuskar kiwon lafiya.