Shugaban hukumar lafiya ta duniyawanda ya gana da ministan kiwon lafiya na Iran Sa’idi Namaki a yau Lahadi ya ce; Yadda Iran take samarwa da ‘yan kasa kiwon lafiya bisa ka’idoji na duniya, wani abu ne wanda ya cancanci yabo da jinjina.

Shugaban hukumar lafiyar ta duniya Tedros Adhanom wanda yake halartar taron da ma’aikatar kiwon lafiya take shiryawa karo na 66, ya ce; Kasashe da dama a duniya suna son ganin sun kwafi salon tsarin kiwon lafiya da Iran din take amfani da shi wanda ya shafi fukkanin ‘yan kasa.

A nashi gefen, ministan kiwon lafiya na Iran Sa’id Namaki ya gabatar da jawabi akan yadda harkokin kiwon lafiya suke tafiya a Iran, sannan ya yi fatan ganin cewa an sami aiki tare a tsakanin Iran din da sauran kasashe da kungiyoyin kasa da kasa a wannan fage.

A yau Litinin ne dai aka bude taron karawa juna sani akan kiwon lafiya karo na 66 wanda kuma zai cigaba har zuwa ranar Alhamis mai zuwa.

Da akwai wakilan kasashe 21 da suke halartar taron da kuma kungiyoyin kasa da kasa a fagen kiwon lafiya