Ali Akbar Zariyan mataimakin musamman ga shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar Iran Ali salihine ya bayyana haka a lokacin da yake bayani wajen bude bukin baje kolin kayayyakin da ma’aikatar nukiliyar kasar ta kera, a birnin karman , ya kara da cewa kashi 100% na na’urorin dahukumar take aikace- aikace da su a cikin gida aka yi su, wannan yasa ta ke tsaye da kafafunta wajen kera duk abin da take bukata ba tare da taimakon wani daga waje ba.

Har ila yau ya fadi cewa mataki na gaba game da samar da ruwa mai kauri a tashar nukiliya ta Arak da aka sake ginawa, za’a fara cin gajiyarsa nan da makwanni biyu masu zuwa, kuma za’a kammala yin gwaje- gwaje nan da watan Mayun shekara ta 2021. Har ila yau ana sa ran nan da shekaru 2 masu zuwa za a fara aiki da cibiyar ta Arak sosai.

Daga karshe ya bayyana cewa babban abin da ya fi muhimmanci akan bututun tace sanadarin urani’um ( centrifuge) shi ne yadda Iran ta samar da tataccen sanadarin urani’um na ( Yellow Cake) wandakowace kasa za ta iya siya , amma babu wanda zai sayarwa da kasar Iran, da yanzu mu muke kera abinmu da kanmu, wanda hakan ya kara mana karfi sosai a matakin kasa da kasa.