Jami’an tsaron kasar sun yi awon gaba da wasu da aka kame dauke da makamai a cikin masu gudanar da zanga-zanga a kasar.

Tashar Presstv ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da jama’a suke gudanar da jerin gwano a jiya a sassa daban-daban na kasar Iraki, domin neman tilast agwamnati ta gudanar da sauye-sauye a cikin harkokin mulkin kasar, an kame wasu daga cikin masu zanga-zangar dauke da bindigogi.

Rahoton ya ce an kame mutum na farko a birnin Najaf ne, bayan da masu zanga-zangar suka lura da cewa yana dauke da bindiga, a nan take suka kame shi kuma suka mika shi ga jami’an tsaro.

Sai kuma mutum na biyu an kame shi ne a birnin Bagadaza, wanda shi ma masu zanga-zangar ne suka lura da cewa yana dauke da bindiga, wanda shi ma ba su wata-wata ba suka damke shi, kuma suka mika shi ga jami’an tsaro.

Tun a cikin makonnin da suka gabata ne dai aka fara gudanar da zanga-zanga a birane daban-daban na kasar Iraki, da ke neman gwamnati ta dauki matakan yaki da cin hanci da rashawa, da kuma magance matsalolin rashin ayyukan yi a tsakanin matasa, lamarin da ya jawo taho mu gama tsakanin masu zanga-zangar a wasu yankuna.