Jami’an tsaron kasar Iraki sun fara daukar sabbin matakai na dawo da doka da odaakasar, bayan da masu zanga-zanga suka fara wuce gona da iri.

Kamfanin dillancin labaran Saumariya News ya bayar da rahoton cewa, a jiya rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta yaki da ta’addanciaIraki ta sanar da cewa, ta fara daukar matakai na tabbatar da tsaro akasar, bayan da lamurra suka fara daukar wani sabon salo da ka iya dagula harkar tsaro a kasar baki daya.

A cikin bayanin, rundunar ta bayyana cewa tana goyon bayan masu zanga-zangar lumana domin bayyana korafinsu, amma kuma ba su goyon bayan ayyukan barna da lalata kaddarorin gwamnati da na al’ummar kasa.

Kafofin watsa labarai da dama a Iraki sun nuna hotunan bidiyo na wasu daga cikin masu zanga-zanga da suke dauke da muggan bindigogi, da kuma yadda masu zanga-zangar suke kona kaddarorin gwamnati da wawushe dukiyoyin jama’a.

A ranar Juma’a da ta gabata ma wasu masu zanga-zangar sun kasha wani babban kwamandan rundunar Hashd Sha’abi Wisan Al-ilyawi, bayan da suka rusa babban ginin rundunar da ke garin Misan a kudancin Iraki, wanda ake ganin akwai hannun makiyan kasar a ciki, inda manyan kwamandojin Hashd Sha’abi suka zargi Amurka da Isra’ila kai tsaye a cikin lamarin.