Iran Da Jamus Sun Jadadda Wajibcin Kawo Karshen Yaki A Kasashen Yemen Da SiriyaShugaban Majalisar Dokokin Kasar Iran Da Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dokokin kasar Jamus sun jaddada wajibcin kawo karshen yaki a kasashen Yemen da Siriya

Kamfanin dillancin labaran Irna ya ruwaito cewa a jiya Talata shugaban majalisar dokokin kasar Iran Dakta Ali Larijani ya gana da mataimakiyar shugaban Majalisar dokokin kasar Jamus Claudia Root a gefen taron 'yan majalisun dokoki na Duniya dake gudana a birnin Belgrade na kasar Serbia, inda ya bayana cewa kasar Iran na adawa da hare-haren kasar Turkiya kan kasar Siriya kasancewa hakan zai janyo hasarar rayuka da kuma yawaitar 'yan gudun hijra.

A bangaren rikicin kasar Yemen kuwa, Dakta Larijani ya ce idan har kasar Saudiya ta amince da warware rikicin Yemen ta hanyar tattaunawa, to kasar iran na iya shiga tsakani domin ganin hakan ya tabbata.

Yayin da ya koma kan kasar Amurka shugaban majalisar dokokin kasar Iran ya ce har yanzu Amurka na tunanin cewa akwai sauran lokaci na tatsan kudi daga mahukuntan kasar Saudiya.

A nata bangare, mataimakiyar shugaban Majalisar dokokin kasar Jamus Claudia Root ta ce kasar Jamus na adawa da harin da Turkiya ke kaiwa kan kasar Siriya.Yayin da take mayar da martani kan tambayar da aka yi mata na cewa me ya sanya har yanzu kungiyar tarayar turai ta kasa yin komai kan hare-haren da turkiya ke kaiwa kan kasar Siriya, Madam Claudia Root ta ce, Turai ta bukaci kasar Rasha da ta yi wa mahukuntan birnin Ankara matsin lamba da kuma dakatar da sayar musu makamai.