Dakarun juyin juya halin Musulunci a kasar Iran (IRGC) sun bukaci dukkan Iraniyawa wadanda suka taba yin aiki, ko suke aiki da Ruhullah Zam, wanda yake ingiza tashe-tashen hankula da suka faru a kasar shekaru 5 da suka su gabata, su bayyana kansu ga dakarun kafin a gane su.

Ruhullahu wanda ya kafa shafin yanar gizo mai suna “Amaad News” ya shiga hannun dakarun na IRGC ne ta wata hanya mai sarkakiya da suka bi don kama shi.

Rahoton ya kara da cewa, dakarun suna da cikakkun shaidu dangane da wadanda suke hulda da Ruhullah Zam da kuma shafinsa a cikin kasar. Don haka suna kira ga duk wanda ya san cewa yana hulda da shi, ya gabatar da kansa ta hanyar wannan adireshin na yanar gizo
contact@gerdab.ir .

Dakarun IRGC sun kara da cewa duk wanda ya gabatar da kansa zai sami sauki a hukuncin da za’a yanke masa. Don sun dade suna bin duddugin wadanda suke adawa da gwamanatin kasar, kuma sun san wadanda suke aiki tare da shi ta shafin nasa ko ta wata kafa.