Wani jami’i a ma’aikatar leken asiri a kasar Iran ya kara fitar da wasu sabbin bayanai dangane da Ruhullah Zam, wanda yake tafiyar da wata kafar sadarwa ta makiya kasar Iran.

A lokacin da yake zantawa da wasu daga cikin manema labarai, jami’in ma’aikatar leken asirin ta kasar Iran ya bayyana cewa, akwai bayanai da dama masu muhimmanci da aka tatsa daga Ruhullah zam, wadanda za su taimaka wajen kara gano wasu daga cikin wadanda suke yin irin aikinsa.

Baya ga haka kuma jami’in ya ce akwai wasu bayanan da aka samu dangane da ayyukan shafin Amad News wanda Ruhullah Zam ya kafa, domin yin zagon kasa da kuma rusa tsarin jamhuriyar muslunci ta Iran, ta hanyar yada labaran karya domin haifar da matsaloli a cikin kasar.

Dangane da yadda aka kame shi kuwa, duk kuwa da cewa ba ya a cikin kasar ta Iran, jami’in leken asirin ya ce sun yi amfani da hanyoyi ne na fasahar zamani ta kololuwa wajen gudanar da aikin, wanda aka shirya shi a cikin sirri kuma aka aiwatar da shi cikin nasara, kuma yanzu Ruhullah Zam yana tsare a hannun jami’an tsaron kasar Iran.