Ministan harkokin wajen kasar Iran Jawad zarfi ya fadi haka ne awata hira da aka yi da shi a wata kafar wasta labarai game da rahoton da jaridar “ New York Times” ta Amurka ta buga inda ta naqalto kasashen Iraki da Pakistan na cewa yarima mai jiran gado na kasar Saudiya ya bukaci kasashen biyu da su yi Magana da kasar Iran kan batun tattaunawa.

Da yake ishara game da kisan kare dangin da Saudiyya ke yi a kasar Yamen ya ce bisa la’akari da irin yanayin da ake ciki babban ci gaba ne, da kasar Saudiyya ta fara tunanin tattaunawa da Iran, don haka idan ta mayar da dukkan batutuwan da suka shafi yankin kan teburin tattaunawaba wai kashe mutane ba to kasar Iran za ta kasance tare da ita a teburi guda.

Har ila yau Zarif ya kara da cewa a kowane lokaci acikin shiri suke wajen bada hadin kai ga makwabtantaa batutuwan da suka shafi tsaron yankin, kuma tuni muka sanar da matsayinmu akai, wanda ko a kwanakin baya ma shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya gabatar wa da babban zauren Majalisar Dinkin Duniya sabbin dabarun tabbatar da tsaro da zaman lafiya a mashigar ruwa ta Hurmuz da ma yankin baki daya.