Mataimakin ministan harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta Iran ya bukaci a gaggauta isar da taimako zuwa kasar Yemen.

A yayin ganawarsa da kakakin kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Muhamad bn Abdul-salam a a marece jiya asabar, mataimakin ministan harakokin wajen kasar Iran Ali Asgar Haji ya tabbatar da dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen sannan ya ce abinda ya fi mahimanci a yau shi ne gaggauta isar da kayayyakin agaji zuwa ga al'ummar kasar Yemen.

Yayin da yake ishara kan kokarin da kasar Iran ke yi na ganin an magance matsalar kasar ta hanyar sasantawa, Ali Asgar Haji ya kara da cewa tun da farko jamhoriyar musulinci ta Iran na adawa da hare-haren zaluncin da kawancen saudiya ke kaiwa kan al'ummar kasar Yemen, tare da kokarin bin hanyoyin siyasa na ganin an dakatar da yakin da kuma killaci kasar, tare da gaggauta isar da taimakon gaggawa zuwa kasar ta Yemen.

Kafin hakan dai, tawagar kasar ta yemen bisa jagorancin kakakin kungiyar Ansarullah ta gana da ministan harakokin wajen kasar Iran Muhamad Javad Zarif, inda suka tattauna kan mahimman batutuwan wadanda suka shafi yankin.

Zarif ya tabbatar da magance rikicin kasar ta Yemen ta hanyar siyasa, tare da nuna goyon bayan jamhoriyar musulinci ta Iran na tsagaita wuta a kasar tare da zama kan teburin tattaunawa tsakanin 'yan kasar ta Yemen domin warware rikicin kasar.