Ma’aikatar harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta Iran ta bukaci kasar Turkiya da ta gaggauwa kawo karshen hare-haren da take kaiwa kan kasar Siriya da kuma janye Sojojinta daga cikin kasar.

Cikin wani bayani da ta fitar a wannan alhamis, ma’aikatar harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta Iran ta bayyana damuwarta kan matakin da kasar Turkiya ta dauka na kai hare-hare kan kurdawan kasar Siriya, inda ta ce wannan kudiri ba wai kawo zai janyo rashin tsaro a Turkiya ba, hakan zai janyo hasarar rayuka da dukiyoyi, don haka kasar Iran na adawa da wannan mataki.

Ma’aikatar harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta Iran ta tabbatar da cewa rikicin dake faruwa a yankin na zuwa ne sakamakon katsa landan din wasu kasashen Duniya musaman ma kasar Amurka,don haka jamhoriyar musulinci ta Iran a shirye take ta bayar da gudumurwarta na ganin an magance sabani dake tsakanin kasashen yankin, musaman ma tsakanin kasashen Turkiya da Siriya, kuma tuni kasar ta fara tuntubar hukumomin kasashen biyu na ganin an warware sabanin dake tsakaninsu.

Sanarwar ta kara da cewa magance sabanin zai tabbata neta hanyar tattaunawa, da kuma yarda da hukokmin kasashen biyu tare da mutunta juna sannan kuma idan bangarorin biyu suka amince da mutunta hurumin kasashe biyu.