Shugaban hukumar kwastam ta Iran da jakadan kasar China a nan birnin Tehran sun tattaunawa kan samar da hanyar saukaka harakokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labaran Iran yahabarta cewa a wannan alhamis, shugaban hukumar kwastam na kasar Iran Mehdi Mir-Ashrafiya gana da jakadan kasar China a nan birnin Tehran Chang Hua, inda suka tattaunawa kan mahiman batutuwa da suka shafi aiki tare na bayar da horo tasakanin ma’aikatar hukumar da kuma bayar da bayyanai da kuma saukaka safarar alhariri tsakanin kasashen biyu, sannan kuma a samar da hanyoyin kasuwanci mafi sauki har 12 tsakanin kasashen biyu tare dabayar da haro gami da korewa tsakanin ma’aikatar hukumomin kasashen biyu.

Mehdi Mir-Ashrafi ya kara da cewa idan ana son ci gaba alakar kasashen biyu, to ya kamata ko wani wata shida bangogin biyu sun zauna kan tebirin tattaunawa domin yin bitar ci gaba da kuma koma bayan da aka fuskanta a tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare jakadan kasar China dake nan birnin Tehran Chang Hua ya yabawa hukumomin hukumar Kwastam na kasar Iran, inda ya ce jamhoriyar musulinci ta Iran na daga cikin manyan kasashe abokanin kasuwancin kasar China da a ko wata shekara ana shigar da fitar da kayayyaki masu yawa tsakanin kasashen biyu.

Chang Hua ya tabbatar da cewa kasar China na bukatar bunkasa harakokin kasuwanci da kasar Iran, sannan ya ce bunkasa alaka tsakanin kasashen biyu na daga cikin mahiman batutuwan da hukumomin kasar China suka sanya a gaba, don haka ofishin jakadancin kasar China dake birnin Tehran zai yi iya kokarinsa na ganin hakan ya tabbata.