Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gargadi kasashen turai wadanda suka rattabawa yerjejeniyar Nukliyar kasar wacce aka fi sani da JCPOA kan cewa lokaci na kure masu, sannan kafar amfani da diblomasiyya tana kara tsugewa dangane da cika alkawulan da suka dauka a yerjejeniyar.

Araqchi ya bayyana haka ne a lokacinda yake zantawa da tokoransa na kasar Rasha Sergei Ryabkov a birnin Mosco a jiya Alhamis.

A ganawarsu na tsawon sa’o’I hudu, Araqchi ya yi ishara ga shawara shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron dangane da yerjejeniyar, inda ya ce shawarar zata yi aiki ne kawai idan an biyawa kasar bukatunta na cikin yerjejeniyar.

Daga karshe ya bayyana cewa idan turawan basu cika alkawulan da suka dauka ba Iran zata ci gaba da jingine yarjejeniyar, daki-daki kamar yadda ta fara.