Iran ta jinjinawa kasar Iraki akan namijin kokarin da ta yi akan ziyarar arba’in na shahadar Imam Husain (a.s)


Ministan tsaron Iran, Birgadiya janar Amir Hatami wanda ya tattauna ta wayar tarho da jami’an kasar Iraqi, ya yi musu godiya da jinjina akan namijin kokarin da su ka nuna dangane da tabbatar da tsaro a yayin tattakin arba’in na shahadar Imam Hussain (a.s).

Daga cikin wadanda ministan tsaron na Iran ya tattauna da su da akwai ministan harkokin cikin gidan Iraqi, Yasin al-Yasiry,babban hafsan hafsoshin sojan Iraqi, Usman al-Ganimy, da kuma shugaban rundunar sa kai ta Hashdussha’abi, Muhandis Abu Mahdi.

A jiya Lahadi ne dai aka kawo karshen ziyarar 40 a karbala wacce miliyoyin mabiya ahlul-bayt (a.s) su ka halarta, daga cikinsu da akwai Iraniyawa fiye da miliyan uku.