Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Iran ta saki yar jaridar kasar Rasha da aka tsare saboda saba dokar shige da ficeKakakin ofishin jakadancin kasar Rasha dake nan birnin Tehran Andre Ganko ya fitar da wata sanarwa a jiya dake tabbata da cewa mahukunta a Iran sun saki Yulia Yuzik yar jaridar nan yar kasar Rasha da aka tsare saboda saba wasu dokokin shedar shige da fice wato Visa, kuma tuni ta bar birnin Tehran zuwa kasar Rasha.

Ya ci gaba da cewa iyalan yar jaridar yan asalin kasar Rasha ne dake da takardar zama dan kasa na kasar Iran, kuma ana zarginta ne da keta dokokin shedar shige da fice na kasar.

Ya kara cewa ba su da masaniya shin ita yar jarida ce ko ’yar kasuwa ko kuma yar yawon bude ido, amma dai an tsare ta ne saboda keta dokar shedar shige da fice wato Visa wanda nan bada jimawa ba za a kammala warware matsalar

Post a Comment

0 Comments

Close Menu