A yau Alhamis ne dai aka yi bikin kaddamar da sabon jirgin saman na bayar da horo wanda aka bai wa sunan; Yasin’ wanda kwararru Iraniyawa ne su ka kera shi dari bisa dari.


Wadanda su ka halarci bikin kaddamar da sabon jirgin yakin sun kunshi; Ministan tsaro, Amir Hatami, sai kuma kwamandan sojan sama Azizi Nasir Zadeh, da kuma mataimakin shugaban kasa akan harkokin kere-kere.

Jim kadan bayan yaye kallabin jirgin, an yi gwaji inda ya tashi sama ya yi shawagi na lokacin mai tsawo.

Jirgin yana da tsawon mita 12 da kuma fadin wasu mitocin 4, sannan kuma yana da nauyin ton 5.5