Jamhuriya musulinci ta Iran, ta ce ba zata rufe ido ba, game da harin da aka kaiwa wani jirgin dakon man fetur din ta a yammacin gabar ruwan Saudiyya ba.

Da yake sanar da hakan sakatare majalisar tsaro ta kasar, Ali Shamkhani, ya bayyana cewa an gano wasu alamu a lokacin da ake binciken faya fayan bidiyon da ake dasu, kuma abunda aka gani shi ne cewa an kai wa tankar man fetur din ta ‘’Sabiti’’ hari ne da makami mai linzami ne.

Mista Shamkhani, ya kuma kara da cwa ire-iren ayyukan ‘yan fashi a teku dake faruwa babban abun damuwa ne ga tattalin arzikin duniya saboda matsalar tsaro a tekun kasa da kasa.

Kafin hakan dai kamfanin man fetur na kasar Iran, (NITC), ya sanar da cewa fashewa abubuwa biyu suka faru ga tankar man, wanda kuma ake kyautata zaton harin makami mai linzami ne.

Saidai kamfanin na (NITC), ya musanta jita jitan cewa an kai wa tankar man hari ne tun daga cikin kasar Saudiyya.