Sakataren majlisar tsaron kasa a IranAli Shamkhani a lokacin ganawarsa daAlxender Lavrentiev manzon musamman na shugaban kaar Rasha Vladimir Putin kan kasar Siriya ya bayyana cewa Iran za ta mayar da martani mai tsanani ga duk wadanda ke da hannu wajen harin da aka kai wa jirgin dakon manta a tekun Red Sea , kuma sai sun yi nadamar abin da suka aikata.

Ya kara da cewa ankai harin ne domin kara ruruta wutar rikici a yankin, kana ya bayyanarashin tsaro a hanyoyin ruwa na duniya a matsayin babban jigon dake haifar da rikice - rikice a yankin.

Idan ana iya tunawa a ranar juma’a da ta gabata ce aka kai hari kan jrgin dakon maina Sabiti mallakin kamfanin dakon mai na kasar Iran, a wani wuri dake da nisan kilo mita 96 daga tashar jirgin ruwa ta saudiyaa birnin jiddakuma harin ya jawo kwarar mai kafin daga bisani a dakatar shi.