Dakarun tsaron kasar Iraki sun kame wata mota shake da makamai da suka hada da bindigogi daban-daban da kuma bamai-bamai a birnin Bagdaza.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto jami'an tsaron kasar Iraki na cewa a jiya asabar sun gano wata mota dauke da makamai da suka hada da bindigogi samfarin Kalashnikova AK-47 da kuma bama-bamai, kuma tuni aka dakatar da direban motar, inda aka fara gudanar da bincike.

Har ila yau sanarwar ta dakarun tsaron kasar Iraki ta ce a jiya asabar din jami'an tsaron kasar sun samu nasarar cabke wasu 'yan bindiga a cikin masu zanga-zanga a birnin bagdaza da sauran biranen kasar.
Rahoton ya ce wasu 'yan bindiga na shiga cikin jerin masu zanga-zangar na kasar Iraki, inda suke yin harbi kan jami'an tsaro da masu zanga-zanga domin kara ruruta wutar rikici.

Wasu manyan 'yan siyasar kasar ta Iraki na daura alhakin abinda yake faruwa a kasar kan wasu kasashen waje musamman Amukra da Haramtacciyar Kasar Isra'ila.