Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Ayatullahi Sayyeed Aliyul Khamina’e, ya bayyana cewa addinin musulunci ya haramta kerewa, ajiyewa da kuma amfani da makaman nukliya, don haka kasar Iran ta haramta yin haka.

Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto Jagoran yana fadar haka a yau Laraba a lokacinda yake ganawa da matasa zababbu daga fannonin ilmi daban-daban a kasar a nan birnin Tehran.

Aya. Khamina’ie ya kara da cewa a duk lokacinda fasahar zamani ta hadu da son iko, to hakan yakan kai mutane ga halaka, kamar yadda makaman nukliya suka zama a duniya a halin yanzu.

Ya ce kasar Iran tana da fasahar kere makaman nukliya amma ta ki kerasu don addinin musulunci ya hana.

A wani wuri a cikin jawabinsa Jagoran ya bukaci jami’an gwamnatin kasar Iran su dauki nauyin matasa wadanda suka yi fice a fannonin ilmi daban-daban, na biyan bukatunsu na karo ilmi da bincike don kada makiya su kodaitar da su zuwa kasashen wajen don neman Karin ilmi.

Har’ila yau Jagoran ya kara da cewa, baya adawa da neman Karin ilmi a kasashen waje, musamman a kasashen yamma da Amurka, amma abinda ba zai amince dashi ba, shi ne daukar mummunan halaye irin wadanda jami’o’in wadannan kasashe suke koyarwa a dawo da su gida.

Daga karshen jagoran yayi fatan cewa nan da kimamin shekaru 50 masu zuwa, harkar ilmi da fasaha za su ci gaba a kasar Iran, ta yadda kasashen duniya zasu aiko da yayansu zuwa nan Iran, don su koyi fannonin ilmi da fasaha da harshen farisanci.