Zanga- zanga ta barke a kasar Bolivia bayan da dan takarar babbar jami’yaradawa a kasar ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa da aka sanar dake nuna cewa shugaban kasar mai ciEvo Morales ne ya lashe.

Magoya bayan shugaban kasar sun yi taho mu gama da magoya bayan dan takarar jam’iyar adawa a kasar Carlos Mesa, da ya kai ga arangama da jami’an yan sanda inda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwasta masu zanga zangar a bbabn birnin kasar La Paz da garuruwan Oruro da Potosi, da Cochanbamba.

Gidan talbijin din kasar ya nuna hotunan wasu masu Zanga- zanga suna cinnawa akwatunan zaben wuta da kuma kona rumfunan zabe a a birnin Tarija , da garin Camiri kuma inda kamfanin iskar gas na kasar yake.

Masu zanga- zangar sun kai hari kan wasu ofisoshi na kamfanin man fetur din kasar.

Sakamakon zaben da aka fitar ya nuna cewa shugaban kasar mai ci Evo Morales ya samu kaso 46.85 % na dukkan kuri’un da aka kada, yayin da Mesa kuma dan takarara jamiyyar adawa ya samu kashi 36.73.

Sai dai jam’iyun adawa sun zargi gwmnati da yin harigidon kuri’u domin taimakawa Morales ya lashe zaben, kuma yayi kira ga magoya bayansa da su fito da dukkan karfinsu domin kare kuri’unsu .