Ayatullah Sayyid Imam Ali Khamnei ya ziyarci rumfuna 30 na baje kolin da manyan kamfanoni masu samar da fasaha su ke yi a nan Tehran.

Kayan da aka baje kolinsu sun kunshi na fagen aikin likitanci da kere-kere wadanda dukkaninsu kamfanonin Iran ne.
Kamfanonin na Iran dai suna aiki ne tukuru domin samar da cigaban da zai fitar da Iran daga dogaro da man fetur a matsayin ginshikin samun kudade shiga.

Jagoran ya shadaiwa mataimakin shugaban kasa a wurin baje kolin cewa; Su yi duk kokarin da za su iya domin ganin ayyukan da matasan kasar Iran din suke yi bai fuskanci matsala ko wani tsaiko ba.