Kamfanin dillancin labarai na AP ya bayyanan cewa jakadan musamman kan zaman lafiya na kasar Amurka Zalmay KhalilZad a karon farko ya gana da wakilan kungiyar Taliban a birnin islam abad tun bayan kasa cimma matsaya a tattunawar da suke yi da kungiyar Taliban da shugaban Amurka ya sanar da suke duk wata tattaunawa da su bayan wani hari a aka kai musu.

Wakilan kungiyar Taliban din sun ki bayyana komai game da zaman na su da ya gudana a birnin Islam Abad na kasar Pakistan saboda basu da hurumin yin Magana akai, rahoton ya ci gaba da cewa duk da bayanan da Washington ke yi na cewa babu wata ganawa da za ta kara gudana tsakanin su da yan kungiyar ta Talib an.

har yanzu tana ganin tattaunar tana da muhimmanci saboda bukatar da take dashi na ganin an kawo karshen yakin da ake yi da kungiyar ta Taliban da ya lakume rayukan dubban mutane tare da jikkata wasu dubban dakuma tilastawa wani adadi mai yawa barin gidajensu ba shiri.

har ila yai rahoton ya bayyana cewa Zalmay Khalil Zad ya isa kasar Pakistan tun a makwannin da suka gabata domin bin kadin ganawar da jami’an Amurka suka yi da pir aministan kasar a bayan taron babban zauren Majalisar dinkin duniya game da muhimmancin komawa kan teburin tattaunawa, inda shi kuma wakilin kungiayr talibin Muallah Baradar ya isa kasar Pakistan domin ganawa da gwamnatin kasar game da wasu batutuwa da suka shafi siyasa da kuma sama da Afganawa 1.5 dake gudun hijira a kasar ta Pakistan.