-KADUNA PRESS.


Rahotannin dake zuwa mana daga birnin tarayyar Nigeria Abuja, sun tabbatar da cewa; jami'an tsaron Nijeriya sun afkawa masu tattakin Arba'in na Imam Husaini na shekarar 1441 yau Juma'a da rana misalin 'karfe 1:53pm.

Tattakin dai sun fara shine daga Masallacin Kwastan (Custom) dake Zone 3.
Kamar yadda suka saba a duk shekara, 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na gudanar da Tattakin Arba'in na Imam Husaini a duk fadin Nijeriya ciki harda birnin tarayyar ta Nigeria wato Abuja domin tunawa da kwanaki 40 da kisan gillar da aka yiwa jikan Manzon Allah, wato Imam Husaini (A.S) a filin Karbala a shekara ta 61 bayan hijira.
Jami'an tsaron sun nuna karfin da ya wuce iyaka matuka gaya wajen tsayar da tattakin, domin sunzo da manyan makamai iri daban-daban, inji majiyar mu.
Ya zuwa hada wannan rahoto, ba a tantance ko mutum nawa aka rasa ba ko kuma aka raunata.
Sai dai majiyarmu ta tabbatar mana da cewa; tun kafin a fara tattakin jami'an tsaro sun cafke wadansu 'yan'uwa Musulmi akan hanyar su ta zuwa  tattakin.
#Tattaki1441.
#ImamHusain.
-KNPRSCD 06.
©KADUNA PRESS.