Jami'an tsaron Nijeriya sun afkawa masu tattakin Arba'in na Imam Husaini na shekarar 1441 a yau Juma'a 18-10-2019 da misalin 'karfe 1:50pm a nan in da a ka taso muzaharar daidai Masallacin Kwastan (Custom) dake Zone 3.

Kamar yadda suka saba a duk shekara, 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na gudanar da Tattakin Arba'in na Imam Husaini a duk fadin Nijeriya, domin tunawa da kwanaki 40 da kisan gillar da aka yiwa jikan Manzon Allah, Imam Husaini (A.S) a filin Karbala a shekara ta 61 bayan hijira.

Sai dai tun bayan ta'addancin jami’an sojojin Najeriya a Zaria a ranar 12-12-2015, almajiran Sheikh Zakzaky, suke fuskantar fin karfi da danniya da take hakkin su daga mahukuntan Najeriya.

bana ma bata canza zani ba, Jami'an tsaron gwamnatin Buhari sunyi dabbacin da suka saba, an fara tattakin ne a jiya Alhamis, inda aka fara daga yankunan Fambeguwa da kuma Kaduna, wanda aka tashi lafiya. Sannan da safiyar yau an yi a yankin Kano wanda masu tattakin suka fuskanci barazanar jami'an tsaro. Amma a karshe an yi lafiya an kare lafiya.

Sannan har wala yau da ranar yau Juma'a aka fara a Abuja. Ya zuwa hada wannan rahoto, ba a tantance ko mutum nawa aka raunata ko kashewa ba.

Sai dai tun kafin a fara ma, jami'an tsaro sun cafke wadansu 'yan'uwa Musulmi akan hanyar su ta zuwa Tattakin.

Isiya-Sy
Kaduna Press