A dare Asabar ne da ya gabata shugaban jam’iyyar ta “ quwwata Lunbaniyya” ya sanar da janye ministocin hudu daga gwamnatin Firaminista Sa’ad al-Hariri saboda zarginsa da gazawa wajen warware matsalolin da kasar take fuskanta.

Jaja wanda ya fitar da bayani akan matakin da jam’iyyar tasa ta dauka ya ce; A yayin da ake tattauna kasafin kudin kasar na 2020, ya bukaci ganin an yi gyare-gyare masu inganci, amma ya fahimci cewa gwamnatin ba da gaske take ba.

Ministocin da suka yi murabus din sun kunshi na aiki, da al’amurran zamantakewa, da kuma mataimakin shugaban gwmanati sai ministar al’amurran tafiyar da mulki.

Kwanaki uku ajere kasar ta Lebanon take fuskantar boren al’ummar kasar saboda karin kudaden fito da haraji da gwamnati ta yi.