Kakkain gwamnan jihar zamfara kan al’amuran tsaro Alhaji Abubakar Dauran ya bayyanawa maneman labarai cewa gwamantin jihar Zamfara ta kira taron gaggawa da shuwagabannin Fulani bayan wani hari da ake zargin Fulani da kai wa a kauyen Sunke dake karamar hukumar Anka, da ya kai ga kashe sojoji 9, tare da jikkata wasu da dama dake kwance a Asibiti a birnin Gusau fadar mulkin jihar ana yi musu magani.

Wannan hari da aka kai shi ne na farko a irinsa tun bayan yarjejeniyar sulhu da gwamnatin jihar ta kulla da masu kai hare hare da yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, sai dai shuwagabannin fulanin sun musanta hannu wani daga cikin magoya bayansu a kai harin, amma sun sha alwashin yin zama da su domin bin kadin wadanda suke da hannu wajen kai harin.

Wasu shedun gani da ido sun bayyana cewa gungun maharan da suka dirarawa dakarun hadin guiwar jamian tsaro sun kai 200 akan babur dauke da manyan makamai a hannunsu.