Rahotanni da suke fitowa daga kasar Yemen sun ambaci cewa; Jiragen yakin Saudiyyar sun kai hari ne a gundumar Hudaidah. 

Tashar talabijin din al-Masirah ta kasar Yemen ce ta bayar da labarin kai harin tare da cewa ya shafi wasu unguwanni na fararen hula.

A gefe daya mai Magana da yawun sojojin kasar Yemen, Yahya Sari’i, ya bayyana cewa; Matukar Saudiyyar ta cigaba da killace kasar Yemen, to za su fuskanci hari mai tsanani a kan cibiyoyi masu muhimmanci na kasar.

Yahya Sari’I, ya cigaba da cewa; Babu yadda za a yi a ce ana Magana akan zaman lafiya sannan kumaa cigaba da killace kasar ta Yemen wanda kuma yake sa fararen hula da dama suna yin shahada.

Yahya Sa’ri’i ya kuma ce; Sojojin kasar ta Yemen za su mayar da martini matukar aka cigaba da kai wa mutanen kasar hari.