Kakakin dakarun tsaron kasar Yemen ya sanar da cewa cikin sa'o'i 48 jiragen yakin kawancen saudiya kan kai hare-haren wuce gona da iri a yankunan daban-daban na kasar sama da 50.

Hukumar gidan radio da talabijin ta kasar Iran ta ruwaito Yahaya Sari'i kakakin rundunar tsaron kasar yemen a daren jiya lahadi na cewa cikin sa'o'i 48 da suka gabata jiragen yakin kawancen Saudiya sun kai hare-haren wuce gona da iri sama da 50 a kasar kuma jihohin Sa'ada dake arewaci da Hijjah dake yammacin kasar sune yankunan dake aka fi kai hare-hare a cikinsu.
Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana irin hasarar rayuka ko dukiya da hare-haren suka janyo ba.

Tun a watan Maris din 2015 ne kasar Saudiya da taimakon hadaddiyar daular larabawa bisa cikekken goyon bayan Amurka ta kaddamar da yakin wuce gona da iri kan al'ummar kasar yemen tare da killace kasar, ta sama da ruwa da kuma ta kasa.

Bisa Alkaluman majalisar dinkin Duniya yakin na yemen yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu 16 da kuma jikkata wasu dubai na daban da kuma raba wasu milyoyi da mahalinsu.