Tashar talabijin din ‘al-mashirah’ ta kasar Yemen ta bayar da labarin da yake cewa; Sojojin Saudiyyar suna cigaba da tafka laifukan yaki akan al’ummar kasar Yemen
Rahoton ya cigaba da cewa;Harin da jiragen yakin Saudiyyar su ka kai ya shafi unguwannin fararen hula a cikin garin Manbah dake gundumar Sa’adaa.

Wadannan hare-haren na Saudiyyar suna zuwa ne adaidai lokacin da mahukuntan kasar suke Magana akan sulhu da zaman lafiya.

Tun a 2015 ne dai Saudiyya ta shelanta yaki akan kasar Yemen da al’ummarta a karkashin kawancen da ta kafa, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci dubban rayukan mutane, tare da jikkata wasu dubbai.

Sojojin kasar Yemen da dakarun sa-kai na “Ansarullah’ sun sha gargadin Saudiyya da cewa idan har ba su daina kai wa kasar hari ba,to za su fuskanci hare-hare akan muhimman cibiyoyinsu.