Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa farashin kayayyakin masarufi ya yi tashin gauron zabi, sakamakon yajin aikin da direbobin manyan motoci suka shiga a kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, yanzu haka lamurra da dama sun tsaya cak musamman wadanda suka ta’allaka da zirga-zirgar manyan motoci tsakanin kasar Kamaru da kuma wasu daga cikin kasashe da ke makwabtaka da ita.

Rahoton ya ce; direbobin sun tsunduma cikin yajin aikin ne domin nuna rashin jin dadinsu dangane da abin da suka kira tauye wasu daga cikin hakkokinsu da hukumomin kasar suke yi, da kuma takura musu daga bangaren jami’an tsaro.

Direbobin manyan motocin dai sun dakatar da duk wata zirga-zirga tsakanin kasar ta Kamaru da kuam kasashen Chadi da Afrika ta tsakiya, inda yanzu haka daruruwan motoci dauke da kaya suke tsaye a kan iyakokin kasashen.

Gwamnatin kasar Kamaru dai tana kokarin ganin ta shawo kan lamrin ta hanyar tuntubar shugabannin kungiyoyin direbobin manyan motocinsu, domin sauraren korafe-korafensu da kuma daukar matakin share musu hawaye.