Shugaba Paul Biya, na Jamhuriyar Kamaru, ya sanar da dakatar da shari’a da ake wa wasu jagororin ‘yan adawa na kasar, daga ciki har da jam’iyyar MRC, ta babban abokin hamayasar a zaben kasar da ya gabata cewa da Maurice Kamto.

A sanarwar da ya fitar a shafinsa na twitter, Mista Biya ya ce ‘’ na dauki matakin dakatar da shari’ar da ake wa wasu jiga jigan jam’iyyun siyasa, ciki har da na jam’iyyar MRC.

Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ma ta tabbatar da hakan, saidai bata fayyace ko dai matakin ya shafi madugun ‘yan adawa na kasar ba, Maurice Kamto, wanda aka cafke bayan zanga zangar nuna adawa da sakamakon zaben shuagaban kasar na 2018 da shugaba Paul Biya ya lashe.

A jiya Juma’a ne aka kammala taron hadin kan kasa a Jamhuriyar ta Kamaru, wanda ake kallon hakan a matsayin wani babban sako daga shugaban kasar na nuna cewa da gaske ya ke wajen hada kan al’ummar kasar.

A ranar Alhamis data gabata ma shugaban kasar ya bada umarnin dakatar da shari’a da kuam sallamar wasu mutane 333 wadanda aka cafke a rikicin dake da nasaba da masu fafatukar a ware na yankin masu Magana da harshen ingilishi.