A karon farko a tarihin Sudan, an nada wata mace a matsayin shugabar kotun kolin kasar.
Neemat Abdullah, ta zama mace ta farko da zata shugabanci wannan kotu a Sudan, a karkashin gwamnatin Abdalla Hamdok.
Ana dai kallon wannan a matsayin wani babban yunkuri na samar da daidaito tsakanin jinsi a wanan kasa a sama da shekaru talatin bayan mulkin shugaba Umar Hassan Al-bashir wanda sojoji suka kifar da mulkisa, bisa matsin lamba na masu zanga zangar kin jinin mulkinsa.
Dama kafin hakan a nada mace ta farko a matsayin ministar harkokkin waje ta kasar.
Ko baya ga Asma Abdallah, ministar harkokin waje ta kasar, akwai wasu mata uku dake rike da mukami a gwamnatin kasar ta Sudan
0 Comments