Shugaban hukumar leken asiri ta Dakarun kare juyin musulunci na kasar Iran hujjatul Islam Hussaini Daib ya sanar da Dakile wata makarkashiyar yunkurin kashe Janar Qasim Sulemani kwamandan Failik Kudus dake karkashin dakarun juyin musulunci na kasar Iran IRGC , wanda ya taka rawa sosai wajen murkushe mayakan kungiyar yan ta’adda ta Da’ash a kasashen Iraki da Siriya.

Hujjatul islami Dai’b ya kara da cewa yan taaddan dake samun goyon baya daga wasu kasashen larabawa da HKI sun yi yunkurin siyan wani wuri dake kusa da Husainiyar Mahaifin Qasim Sulemani, inda zasu dasa wani abin fashewa domin tarwatsashi a lokacin zaman makoki na ranekun Ashura da Tasu’a na shahadar Imam Hussaini a ranar 8-9 ga watan satumba da ya gabata.

ya kara da cewa Ya zuwa yanzu an cafke mutane 3 da ake zargin suna da hannu wajen shiryar kai harin, shekaru ke nan wasu kasashen larabawa da HKI suke ta kulla makarkashiyar ganin an kashe Janar Qasim Sulaimani .