Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin kasar Masar ta amince ta tattauna da kasashen Habasha da Sudangame da takaddamar da ake yi kan tekun Nilu bayan da shugaban kasar Habasha da ya samu lambar yabo ta Noble ta zaman lafiya abaya bayan nan, ya sanar da cewa ba zai dakatar da ci gaba da aikace - aikacen gina madatsar ruwa da yake yi a kasar.

Kasar ta Masar ta amince da gayyatar da Amurka ta yi mata na ganawa da kasashen biyu, bayan da ta bukaci masu shiga tsakani na kasa da kasa da su sanya baki wajen ganin an kawo karshen takadamar da aka kwashe shekaru9 ana tattaunawa akai, ba tare da cimma wata matsaya ba.

Dukkan kasashen biyu suna da sabani game da gina madatsar ruwan da Habasha take yi.

Masana na bayyana damuwarsu na yi yuwar afkuwar rikici tsakanin kasashe 3 dake makwabtaka da kogin na Nilu matukar ba’a cimma matsaya ba kafin fara aiki da Madatsun ruwa nan da farkon shekara mai kamawa.