Ma’aikatar harkokin tsaron kasar Rasha ta ce; ba ta da cikakken bayani akan cewa harin da Amurka ta ce ta kai a Syria ya yi sanadin mutuwar Abu Bakar al-Bagadadi.

Jami’in ma'aikatar tsaron kasar Rasha Majo Janar Igor Konashenkov ya fadawa kamfanin dillancin labarun RIA cewa; Ma’aiakatarsa ba ta da cikakken bayani akan harin da sojojin Amurkan su ka kai a yankin Idlib inda su ka iya kashe shugaban Da’esh al-Bagadadi.

Bugu da kari, sojan na Rasha ya karyata cewa kasarsa ta taimakawa Amurkan akan farmakin da ta kai, kayar yadda shugaban kasar Amurka ya riya