Tashar talabijin din “Rusia Today” ta kasar Rasha ta ambato ma’aikatar tsaron kasar Turkiya tana cewa; Babu bukatar sake kai wasu sabbin hare-hare a arewa maso gabashin kasar Syria.

A wani bayani da ma’aikatar tsaron kasar Turkiya ta fitar da safiyar yau Laraba, ta bayyana cewa;Amurka ta sanar da Turkiya cewa mayakan kungiyar kurdawan Syria sun janye daga yankin da aka cimma yarjejeniya a tsakanin Turkiyan da Amurka.”

Tun a makon da ya shude ne dai Turkiya ta bai wa kungiyar Kurdawan Syria sa’o’i 120 da su fice daga yankunan da suke da iyaka da ita.

A jiya Talata an yi ganawa a tsakanin shugabannin kasashen Turkiya da na Rasha, inda bangarorin biyu su ka tattauna halin da ake ciki a arewacin kasar ta Syria.